Hukumar Dake kula da watsa labarai NBC ta haramta Saka wakar Ado Gwanja a radio da talabijin

hukumar Dake kula da watsa labarai ta Nigeria ta haramta Saka wakar fitaccen mawakin kannywood Ado Gwanja a gidajen radio da talabijin

 

 

A jiya ne dai hukumar NBC ta sanar da haramtawa kafatanin gidajen radio Hadi da talabijin Saka wakar Ado Gwanja Mai suna warrr a fadin Nigeria

 

 

Wannan ya biyo bayan samun umarnin gaggawa da wata kotun musulunci tayi a kama wasu mawakan kannywood Wanda suka Hadar da Ado Gwanja, safarau, 442 murja , kawu Dan sarki da dai sauran su

 

 

Hukumar dai ta bayyana cewa duk gidan radio ko talabijin da suka samu da karya wannan doka toh babu shakka zai fuskanci fushi hukumar

 

 

Daga cikin dalilan da hukumar ta fitar ta bayyana cewa mawakin yayi amfani da kalaman rashin tarbiyya a cikin wakar tasa Wanda Hakan ba karamin laifi bane , dilole tasasu daukar wancen mataki akan wakar tasa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button