Yan Kannywood Suna Kokarin Ganin Baya na- Don na Maka su A Kotu -lauya A Kano

Yan Fim Kannywood Suna Kokarin Ganin Baya na Don Sun Maka Ni A Kotu Saboda Na Ce Suna Bata Tarbiyya Cewar Dan Jarida Indabawa Aliyu Imam

 

 

A daren jiya aka yi sallama da ni bayan na fito ne sai mutumin ya ce daga Kotu ne aka aiko shi waje na da sammaci Ya ba ni wasu takardu cewa wai wani Mutum mai suna Hamisu Lamido Iyantama ne ya yi kara ta

 

 

saboda na yi rubutu kan yan fim na ce suna lalata tarbiyya kuma Iyantama dan fim din ne sannan na yi rubutu na nuna rashin jin dadi na sanda wani Sanata mai suna Barau Jibril ya raba wa yan fim motoci babura kyamarori kwamfuyutoci da kudade alhalin mabukata suna mutuwa a asibiti saboda rashin kudin magani
wasu na mutuwa saboda yunwa

 

 

 

 

Sannan ina goyon bayan Gwamna Ganduje ina adawa da Barau Jibril sanda shi Barau din ke takun saka da Baba Ganduje a kungiyarsu ta G7 Wannan shi ne kadai laifina

 

 

Bin tafarkin Annabi (SAW) na umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da yaki da rashin tarbiya ya zama laifin da har ake kokarin a ga bayana me na aikata ma shi wanna shine laifin da ake tuhuma ta akai

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button