yan’ bindiga Masu garkuwa da mutane sun kama barawo dake yi masu sace-sace a gidajensu

Karfin hali sata a gidan yan’ bindiga Masu garkuwa sun kama barawo dake yi masu sace-sace a gidajensu

 

 

Wasu gungun yan bindiga a kauyen Kilili na jihar Katsina sun kama wani matashi da suka ce barawo ne dake zuwa gidajen su yana yi masu barna yana sace karafuna da sauran kayayyaki a gidajen su

 

 

 

A wani bidiyo da aka ga yadda yan bindgar suka daure matashin mai suna Halliru wanda ya ce shi dan kauyen Ranka ne sannan suka gabatar dashi ga yan jarida kafin daga bisani suka mika shi ga hukumar soji domin a dauki mataki akansa

 

 

 

 

Alh Usman Kachalla Rugga shine shugaban yan bindigar wanda ya shaidawa wani mutum cewa dama sun dade suna neman kama masu zuwa suna yi masu sace-sace a gidajen su sai gashi yau Allah ya basu sa’a sun kama ɓarawon

 

Ya ce sunyi niyyar kashe shi to amma suka yanke shawarar gayyatar yan jarida cikin dajin domin nunawa Gwamnati irin kokarin da suke yi wajen kama baatagari kuma yanzu zamu baku shi a kaishi wajen hukuma su hukunta shi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button