Wani abu da baku sani ba game da rayuwar Momi Gombe jarumar kannywood

Wani abu da baku sani ba game da rayuwar Momi Gombe akan rayuwar ta da baku sani ba ta bayyana yana mana yadda ta fara harkar Film

 

Sunana maimuna abubakar wacce aka fi sani da momi gombe actress a matsana’antar kannywood an haife ni a garin gombe anan nayi primary school dina anan nayi secondary school dina dukkanin rayuwata a garin gombe nayi sai yanzu kuma sana’a ta maida ni garin kano

 

Momi suna ne da na gada a wajen kakata maman baba na ana kiranta maimunatu to su kuma baza su iya kiran sunan ba shi yasa baba na yake kira na maimunatu

 

 

 

 

 

Mutane da yawa suna kira da hakan tabbas munyi wakar Jarumar mata da Hamisu Breaker abokin aiki na Ina farin ciki da wakar domin ban yi tsammanin zata kai wannan mataki da ta kai ba

 

 

Ta hannun mai gida na Usman Mu’azu na shiga Film usman ya kasance dan garin Gombe ne kuma yana zuwa har cikin gidan mu kuma yasan yan uwana iyaye na da kakanne na kuma ya zama kamar dan gida a lokacin ni kuma ina sha’awar yin Film

 

 

idan suna aikin su na film a gida ana saka ni na kai musu abinci idan na kai abincin sai na zauna nayi ta kallon su sai watarana nace masa ina so nima na shiga masana’antar kannywood sai yace ai iyaye na baza su barni ba sai nace idan kayi musu magana ai zasu barni da ya lura ina so film sosai sai yayi magana da mama ta kuma sai ta barni na fara film

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button