Abba Kyari Ya Musanta Zargin Mallakar Kadarori a fadin nigeriya da duniya baki daya

Abba Kyari Ya Musanta Zargin Mallakar Kadarori ya musanta zargin da ake masa na handama da babakere na gukiyar kasa

 

 

Lauyoyin dake kare mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari sun musanta zargin da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta yi na cewa ya ki bayyanna wasu manyan kadarorin da ya mallaka

 

 

A wata sanarwa da lauyansa Barista Hamza Dan tani ya san ya wa hannu ya ce ‘An ja hankalin mu kan wani labari da wasu jaridun kasar suka wallafa ranar Litinin inda suke cewa gwamnati ta gano wasu manyan kadarorin Abba Kyari 14 da suka hadar da manyan kantunan sayayya da filin wasan polo da gidaje da gonaki

 

 

 

 

A cikin Sanarwar lauyan ya musanta wannan ikirari yana mai cewa sun fahimci hukumar NDLEA na son bata wa Abba Kyari sune ne ta kowane hali saboda a cewarsa har yanzu mutanen Najeriya na goyon bayan tsohon jami’in dan sandan

 

 

Wanna tasa wasu mutane ke kokarin sai sun goge wanna abun da yan Nigeria ke fadi a kan hazikin dan sanda Abba Kyari haka kuma ba dai dai bane duk da su yan kasa sun yarda da irin namijin kokarin da yake a bakin aikin sa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button