Abubuwa 17 da zan yi idan PI-NETWORK ta fashe – wani matashi

Abubuwa 17 da zan yi idan PI-NETWORK ta fashe

 

 

1. Zan gina katafaren gida na Miliyan 500 a Kano sannan in gina gidan Bilyan 100 a Abuja

 

2. Zanje Banana Island na sayi gidan bene 🏢 me hawa 50 kamar na Bilyan 50

 

 

3. Daga lokacin da ta fashe na dena taka qasa sai dai kafet kuma idan na taka nawuce shikenan sai dai a nemo sabo

 

 

4. Zan siyi jirgin sama guda 150 a dinga yi mini haya da su

 

5. Zan sayi Prado baka da fara da ja da koraye da blue da ruwan kasa

 

6. Zan siyi 4matic guda 36 adadin yawan jihohin Najeriya wato kenan duk jihar da zanje zan hau daya idan naje nagama uzurina zan barta acan

 

7. Idan na tashi aure za a diba dangina da dangin amarya a harbamu duniyar wata sai anyi shekara takwas ana shagalin biki na a can

 

8. Zan gina gidan mai mai kan fanfo 10,000 aduk jihohin Nigeria

 

9. Zan je London na gina Estate

 

10 A Dubai kuma hotel din Bilyan 900 zan gina

11. Zan sayi rijiyar man fetur guda 30 a Nigeria

 

12. Sannan duk wanda muka hadu dashi zan bashi kyautar dubu dari 500

 

13. Zan siyawa abokaina motocin hawa kowannensu kamar guda 100 alaji

 

14. Zan je unguwar su budurwata nasa a rushe gidanjen layin ayiwa kowa gidan miyan 100

 

15. Idan na kwanta a cikin gida shikenan sai dai na bayar dashi kyauta saboda ba zan kara kwantawa aciki ba

 

16. Zan rabawa kowane dan Afrika kudi kamar naira milyan 5 Biyar haka

 

17. Sannan zan siyawa kowane dan garimmu mota ta milyan 100 saboda sune dangina

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button