Video Yadda Za’a kai wata amarya akan Babur Mai Kafa 2

GARAB’ASAR DA KE A CIKIN AUREN BAK’AUYIYA

 

Bincike ya tabbatar kuma duniya ta sheda cewa matan kauye sun fi kowace mace dadin zama domin su da gaske suke zaman auren babu son kudi ko son kyale kyaletun duniya babu bani-bani balle a ji kansu da miji, ga aurensu babu wani lefe

 

 

Bugu da qari duk abin da ka kawo gidanka shi zata dafa maka ko da dawa ce miya in dai taji daddawa da farin magi ta isheta ba dole sai da naman miya ba kuma a haka zaka ji girkinta akwai dadin d’and’ano

 

 

Da ita ake zuwa noma ko kiwo ita ke yo itace tayi surfe tayo nik’a tayi bakace kuma ita zata dafa ta kai gona mijinta da ‘ya’yanta su ci wanki da zuwa rafi duka ita c

 

 

Wata fa’ida da alfanun auren bak’auyiya shine sam bata san wani abu wai shi ‘yanci ba ita kawai ta tashi ta ga gyatumarta tana ta bautawa gyatuminta bilhakki da gaskiya kuma suna ji malamai suna cewa aljannar mace tana a qasan tafin qafar mijinta saboda haka ido rufe suke neman aljannarsu a gidan auren su

 

 

 

Malam auren bak’auyiya duniya ne idan har kana son ka rayu a gidan ka kamar wani sarki to ka tafi kauye ka auro bak’auyiya abinka idan ka aurota ka koya mata ABC da Alifun-ba’un da karatun sallah ka dai karkad’e mata duhun jahilcinta

 

Sai dai kai kuma kaji tsoron Allah kada ka danne mata hakki kuma ka rage mata wahalhalun aikin cikin gida kuma watarana ka zagaya da ita ta ga birni ka dan saya mata shawarma da Rufaida yoghurt domin itama taji dadi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button