Video Yadda Yan Bindiga Suka Kai Hari Wani Gida A Funtua Don Sace Mutane

Yadda Yan Bindiga Suka Kai Hari Wani Gida A Funtua Don Sace Mutane Amma Suka Gamu Da Bakin Ciki

 

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kutsa gidajen mutane a Funtua a daren ranar Juma’a sun sace wasu amma sun gaza shiga wani gida domin yin abun da suke so

 

Wani faifan bidiyo da aka nada da na’urar daukan bidiyo na sirri ta CCTV ta nuna yadda yan bindigan suka so shiga wani gida amma suka kasa

 

 

 

Wani abokin mai gidan da suka kasa shigan ya ce mai gidan da iyalansa suna Abuja amma ya hada na’urar ta CCTV da wayarsa don haka ya ga abin da ya faru

 

 

Yan bindigan wanda bisa alamu sun so sace wasu ne sun taho kauyen misalin karfe 10 na dare kuma suka fara kutsa gidaje suna sace mutane

 

A cewar Ahmed Abdulkadir abokin mai gidan (an boye sunansa) bayan sun yi harbi a kofar, sun shiga cikin gidan amma ba su tarar da kowa ba Allah ya tsallakar da masu gidan basa garin a lokacin

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button