Video Mata da mijin da suka yi fice a waƙoƙin Annabi a tare

Mata da mijin da suka yi fice a waƙoƙin Annabi tare

 

Duk da tarin mawaƙan yabon Manzon Allah Annabi Muhammadu S.A.W. da ake da su a ƙasar Hausa da duniya baki ɗaya ba kasafai ake samun mata da miji na yin yabon a tare ba

 

 

Wannan ta sa Hafiz Abdallah da matarsa Murja Bukhari Adam wadda wasu ke kira da sunan mijinta suka yi fice a fagen waƙoƙin yabon Annabi

 

 

Ma’auratan waɗanda ‘yan asalin Jihar Kano ne malami ne da ɗalibarsa kafin su yi aure amma yanzu sun zama mata da miji inda suke da ra’ayi iri daya

 

 

 

Ni ɗalibarsa ce tun a Islamiyya yake ban ƙasidu kuma da Allah ya tashi ikonsa sai ya haɗa wani abu mai girma shi ne aure kamar yadda Murja ta shaida game da mijinta

 

Baya ga waƙa Hafiz ya ce yana yin harkoki da dama ciki akwai sayar da tufafi da harkokin man fetur da kuma dillancin tafiye-tafiye.

 

An haife shi a unguwar Kwanar Ɗiso da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a birnin Kano, kuma a nan ya taso.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button