‘Na Kashe Iyayena Ne Saboda Sun Yi Batanci Ga Annabi SAW shi yasa ya kashe su

‘Na Kashe Iyayena Ne Saboda Sun Yi Batanci Ga Annabi SAW shi yasa ya kashe su

 

Wani matashi mai suna Munkaila Muhammad mazaunin ƙaramar hukumar Gagarawa dake jihar Jigawa ya kashe iyayen sa ya kuma bayyana dalilin kashe su da cewa saboda sunyi kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad SAWA

 

 

Matashin wanda ya kasance mawaƙi kuma mabayin ɗariƙar Tijjaniyya yace iyayen sa suna sukar sa da kiran sa mahaukaci sannan suna inkarin wakokin sa da yake yi na yabon Manzon Allah

 

 

 

yadda yan sanda suka kama matashin mai shekaru 37 bayan ya kashe iyayen sa sannan ya raunata wasu mutane 2 a ranar Alhamis

 

 

Ya yi amfani da taɓarya wajen kashe mahaifinsa Ahmad Muhammad mai shekaru 70 wanda shi ne Sarkin kauyen Zarada da ke yankin karamar hukumar Gagarawa da mahaifiyarsa Hauwa’u mai shekara 60

 

 

A wani faifan bidiyo da aka nada a hannun yan sanda da suka dauka Munkaila ya ce bai yi nadamar abin da ya aikata ba domin an umarce shi da ya yi hakan

 

Na kashe su ne saboda sun ki yarda da gaskiya game da Annabi Muhammad (S. A.W.A) Na kashe su ne saboda zagin Annabi kuma hukuncinsu kisa ne babu tuba ga duk wanda ya zagi Annabi

 

 

Ni mawakin yabo ne ga Annabi bana nake niyyar yin bidiyon waka ta kuma in sha Allahu zan yi haka zan samu yanci na za a sake ni domin Allah yana tare da mai gaskiya shi ya sa ban damu ba akan matakin da na ɗauka in ji Munkaila a wani faifan bidiyo da ‘yan sandan suka dauka

 

 

Iyayena (ba sa son Annabi Muhammad) saboda ina girmama shi sun kira ni mahaukaci na roki mahaifina ya tallafa min akan aikin da nake yi (wakar yabo) kuma na ce masa ba na neman mata bana caca bana shan miyagun ƙwayoyi kuma ba na yin sata amma ya ƙi

 

Mahaifiyata takan je garuruwan da ke makwabtaka da ni domin ta bata min suna tana gaya wa mutane su ƙi ni a duk lokacin da na zo wakar yabon Annabi saboda mahaukaci ne ni kuma na ki yin aikin noma a gona

Yanzu ina hannun yan sanda saboda a tunanin dan Adam na yi abin da bai dace ba amma a wurin Allah da Annabi abin da na yi shi ne daidai in ji Munkaila

 

Munkaila wanda yake da ya’ya biyar ya ƙara da cewa yana zargin mahaifinsa da yin lalata da matarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button