An Sauyawa ‘Ya’yanta Suna Daga Zainab Da Halima Zuwa Deborah Da Sera Bayan An Sace Su

An Sauyawa ‘Ya’yanta Suna Daga Zainab Da Halima Zuwa Deborah Da Sera Bayan An Sace Su Aka Mayar Da Su Kiristoci

 

 

Wata baiwar Allah yar asalin jihar Sokoto dake zama a garin Osogbo dake jihar Osun ta koka da yadda wata mata Bayarabiya ta sace mata ‘ya’ya ta sauya musu addini ta karfi da yaji inda ta tattara su ta kai jihar Lagos

 

 

Matar ta koka kan hakan ne a wani bidiyo inda ta bayyana cewa matar ta yi amfani da jinyar rashin lafiya da take yi ne bayan rasuwar mijinta inda kafin ta dawo daga jinya ta gudu da yaran

 

 

 

Yanzu haka bayan an ceto yaran bisa jagorancin Sarkin Hausawan Olanta dake Adamo a yankin Ikorodu dake jihar Lagos an sauya musu suna daga Halima zuwa Deborah inda ita kuma dayar ta koma Sera daga Zainab

 

Yanzu dai an kama ita wanna ɓarauniyar yaran domin a hukunta ta yadda ya kamata dama irin wanna suna daya a cikin mutane sai an saba da su sai su dinga yiwa mutane sata kudi ko kaya ko kuma ɗaukar yara

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button