Abin da ya sa na yi rawa da ‘yan mata a dandali – Tahir Fagge

Abin da ya sa na yi rawa da ‘yan mata a dandali – Tahir Fagge

 

A karon farko fitaccen jarumin finafinai Hausa Tahir Mohammed Fagge ya fadi dalilin da ya sa ya yi rawa tare da wasu matasan mata a bainar jama’a a wajen wasan gala

 

 

Tun a farkon 2020 ne aka fara yaɗa bidiyon rawa da waƙar da Tahir ya yi tare da matan a wani wasan gala inda aka gan su suna bin wata waƙar Hamisu Breaker Ɗorayi to amma bidiyon bai haifar da surutai ba sai a bana lokacin da aka ƙara wallafa shi a soshiyal midiya musamman a TikTok da YouTube

 

 

Da yawa waɗanda su ka kalli bidiyon sun ce jarumin bai kyauta ba da aka gan shi ya na rawa da yaran mata sa’annin jikokin sa

 

 

 

Sai dai a tattaunawar da ya yi mujallar Fim kwanan nan Tahir Fagge ya kare kan sa tare da yin kakkausan martani ga masu cewa abin da ya yi bai kyauta ba

 

 

Ya faɗa wa mujallar cewa ya na jin duk maganganun da ake yi a ciki da wajen masana’antar dangane da bodiyon Daga nan ya ɗauko bayanin yadda abin ya faru tun daga tushe

 

 

 

Lokacin da abin ya faru ina kwance ne a gida ba ni da lafiya na samu matsalar cutar shanyewar ɓarin jiki har ya zama ba zan iya tafiya mai tsayi ba a lokacin har sai na zauna na huta Kuma ba ni da kuɗin da zan je asibiti kuma ina neman kuɗi N260,000 wanda da shi ne za a ɗauki hoton zuciya ta za a ɗauki hoton ƙirji na da yi mani magani

 

Yaran nan su ka zo har gida su ka same ni su ka ce ko da ba zan yi rawa ba su na so na je wajen na zauna a matsayi na na babban baƙo Kuma a nan su ka ɗauki kuɗi N160,000 su ka ba ni. Ka ga saura N100,000 kenan wanna tasa naji dadi sosai

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button