YADDA MUKA KUƁUTA DAGA HARIN YAN BINDIGA Sheikh Gurutum

YADDA MUKA KUƁUTA DAGA HARIN YAN BINDIGA Sheikh Gurutum

Fitaccen malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya bayyana yadda ya kubuta shida tawagar sa daga harin yan bindiga

 

Malamin ya bayyana haka ne yayin karatun da yake gabatarwa inda yace Allah ne ya ƙwace su a wannan lokacin

A cewar malamin lokacin da suke kan hanya suke tafiya ƴan bindigar sun tare su inda suka zo wajan motar da nake ciki inji Malamin

Yace da suka zo sun nemi da mu bude motar mu muka ƙi suka ƙara cewa mu buɗe motar mu idan ba haka ba za su buɗe mana wuta to a lokacin dukkanin mu mun yanke cewa baza mu bude motar Ba

Ana cikin wannan yanayi ne kwatsam sai mota daga cikin ayarin mu da ke can baya ta juya da nufin komawa da baya domin ta gujewa hari

Sanadin wannan yasa hankalin ƴan bindigar ya koma kan motar da ke kokarin tserewa inda suka bita da harbi to ganin waccan mota ta ɗauke musu hankali yasa direban mu ya fizgi motar mu a guje tare da ayarin motocin da muke tare dasu

Malamin ya bayyana cewa duk cikin ayarin mu babu wanda aka kama ko yaji wani rauni dukkanin mu Allah ya tseratar damu Allah ya kara tsare dukkanin musulmin duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button