Wakar Ado Gwanja CASS ta zama annoba ga yan mata marasa tarbiya

Wakar Ado Gwanja CASS ta zama annoba ga yan mata marasa tarbiya masu son lallai su sai sun nunawa duniya basu da mutunci kuma basu da tarbiyya

 

 

Duk macen da take bin wakar Ado Gwanja CASS ya kamata ta sani bata yiwa iyayen ta adalci ba kuma bata kyautawa ya’yan da zata haifa ba idan tayi aure idan kuma mai aurece bata kyautawa jikokin da yayan ta zasu haifa ba

 

 

 

Duniya dai makarantace lahira wajen hisabi anan zata ga sakamakon da ta aikata me kyau ko mara kyau kuma lahira gida 2 ne Aljannah ko Wuta wa’iyazubillah.

 

 

 

 

Annabi S.A.W ya bamu labari Lokacin da ya leka wuta sai ya ga mafiya yawa a cikinta mata ne ya Subhanallah yar uwa yi kokari ki kubutar da kanki daga shiga wuta

 

 

Domin kuwa lallai a cikin wanna gidajen guda biyu dole ne sai mutum ya tsinci kan sa a cikin daya ne zai haka yan uwa mu guji duk abin da Allah baya so muyi abun da yake so domin mu tsira da rahamar sa ranar alkiyama Allah yasa mu dace

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button