A’isha Humaira ta mayar da martani akan zagin da ake wa uban gidan ta Dauda kahutu rarara

A’isha Humaira ta mayar da martani zagin da ake wa uban gidan ta Dauda kahutu rarara inda take mayar da raddi ga masu zagin shi a kan kyaututtukan da ya raba

 

A’isha Humaira jarumar Kannywood, kuma yarinyar Mawaki kuma Jarumin masana’antar shirya finafinai ta kanywood Dauda kahutu rarara ta mai da zafafan martani ga wasu da suke Zagin uban gidan nata

 

Raba motoci da wayar iPhone da kudi da rarara yayi ya bar baya da kura inda wasu da basu sami nasarar samu wanna gasar ba suke Zagin shi uban gayyar wato Dauda kahutu rarara kenan suna zargin sa da rashin adalci da yayi masu

 

 

 

 

Sai dai kuma haka na faruwa daya daga cikin manyan yaran nashi ta fito tana maida zafafan martani ga masu wanna Zagin ta bayyana rashin jin dadi abun da ake fada a kan uban gidan nata wanda kuma masu zagin basa faden alkairin sa

 

 

Hakan yasa itama take mayar da raddi da nuna rashin jin dadi abun da ke faru wanda wanna gasar shi yaga dama yasa kuma sai hakan ya zama abun tsiya haka dai take fada kamar bazata dena ba

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button