Cikakken video yadda Gini ya Danne Yan Kasuwa a Jahar Kano

Ƙungiyar Marubutan Arewa “Arewa Media Writers” Tana Jajantawa Ƴan Kasuwar Kantin Kwari Dake Jihar Kano, Bisa Iftila’in Ambaliyar Ruwan Sama Da Yayi Ɓarna A Kasuwar

 

 

 

…Haka zalka ƙungiyar tana jajantawa ƴan kasuwar waya na “Beirut Road” bisa Iftila’in da ya faru na ruftowar gini wanda hakan yai sanadiyar mutuwar wasu da raunata wasu da dama wanda har yanzu ba’a gama tantance adadinsu ba.

 

 

 

Ƙungiyar Marubutan Arewa “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, da shugaban ƙungiyar na jihar Kano Comr Umar Kabir Dakata, suna miƙa saƙon jajantawa ga ƴan kasuwar kantin ƙwari musanman waɗanda Iftila’in ambaliyar ruwan sama ya shafi shagunan su, sakamakon mamakon ruwan sama.

 

 

 

Haka zalika ƙungiyar “Arewa Media Writer” tana ƙara jajantawa ƴan kasuwar waya na “Beirut Road” bisa Iftila’in da ya rutsa na ruftowar gini wanda hakan yai sanadiyar mutuwar wasu da raunata wasu da dama wanda har yanzu ba a gama tantance adadinsu ba.

 

 

 

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” tana kira kira ga Gwamnati da masu ruwa da tsaki dasu taimakawa mutanen da wannan Iftila’i ya shafa, ta basu gudunmawar da ta dace domin sauƙaƙa musu raɗaɗin abinda ya same su.

 

 

“A ƙarshe ƙungiyar “Arewa Media Writers” tana Addu’ar Allah ya kare afkuwar hakan a gaba, ya mayar masu da mafi Alkhairin abinda suka rasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button