Yadda Ake cigaba da rikici da Ado Gwanja kan sabuwar wakar sa:an fara zama a kotu

A cigaba da rikicin da akeyi da shahararran mawakin Kuma jarumin kannywood Ado Gwanja, mun samu labarin cewa mawakin ya mayar da martani kan lauyan da ya shigar da shi Kara

 

 

Indan Baku manta ba dai an shigar da Ado Gwanja lakabin limamin mata Kara a gaban kotu inda ake so kotu da ta Hana mawakin sakin sabuwar wakar Mai suna chass lakabin asosa

 

 

Lauyan dai ya Kara da cewa mawakin na amfani da waka wajen Bata tarbiyyar ya’ya mata musamman hausawa inda yake shigo da wasu kalar rashin tarbiyya cikin su

 

 

 

 

Sai dai anashi bangaren Ado Gwanja ya yayiwa lauyan martani inda yake cewa shifa sanar are sa ce waka Kuma babu Mai hanasa Yin waka

 

 

Ya Kara dacewa batun rashin tarbiyya da lauyan yace suke koyawa mata wannan ba gaskiya bane inda Gwanja yace sunfi malamai isar da saki zuwa ga Al umma

 

 

Wannan martani da Gwanja yayi ya matukar tinzirah wasu matan inda suka shiga kafafen sada zumunta suka fara yiwa lauyan martani da akyale musu mawakin su ya cigaba da basu nishadi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button