Anyi Garkuwa Da Safara’u Mawakiyar Da Take Tashe A Yanzu’ – Datty Assalafy

Tabbas Hakane Anyi Garkuwa Da Safara’u Mawakiyar Da Take Tashe A Yanzu’ – Datty Assalafy

Biyo Bayan Cece Kuce Da Wakar Wata Matashiyar Budurwa Mai Suna Safiya Yusuf Yake Janyowa A Yanzu, Wanda Wasu Suke Kallon Wakokin Da Rushe Tarbiyya Ko Kuma Yada Badala.

Idan Kuna Bibiye Damu,Zaku Ga Muna Saka Muku Labarai Dangane Da Wannan Matashiyar Mawakiyar Wato Safara’u Da Tauraruwarta Take Haskawa A Yanzu, Yadda Muka Dauko Wani Tsokaci Daga Shafin Marubuci Akan Al’amuran Yau Da Kullum Wato Datty Assalafy.

Yadda Bayaninsa Ya Fara Da Cewa:
‘LABARIN GASKIYA NE AMMA BASU ARCE DAGA KANO BA

Na ga wani labari da aka yada a jaridar Rariya cewa Shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano Ismail Na’abba Afakallahu ya bayyana cewa yanzu haka suna neman Mista 442 da Safara’u ruwa a jallo.

To banyi kasa a gwiwa ba, na sa wani aminina da na san yana da kusanci da shugaban hukumar tace fina-finan ya min bincike don tabbatar da sahihancin labari, kuma sakamakon bincike ya tabbatar da gaskiyar labarin, ana neman su za’a kama yanzu hakaSai dai jawabin shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano yace 442 da Safara’u sun gudu daga jihar Kano, saboda dokar jihar Kano ba za ta ba su damar yin abinda suke so na bata tarbiyya ba, a rahoton jaridar Rarayi kenan.

Rubutun da nayi dazu akan wadannan bayin Allah yayi tasiri sosai, abu biyu ne aka fi mayar da hankali a kai, Shine wai basa zama a Kano, kuma wai 442 bai yi
garkuwa da Safara’u baTo batun cewa basa Kano ba gaskiya bane, na rantse da girman Allah shekaran jiya wani abokina amasana’antar Hausa film ya ga 442 da daddare awani hotel dake cikin birnin Kano

Wato ba jimawa 442 ya san cevwa Hisbah zasu iya kamashi, don haka sai ya shiga yin basaja yana badda sawu tare da wofantar da hankalin mutane, yana cewa shi ya ma koma Abuja da zama, alhali Wallahi karya ne, zamansa yafi yawa a Kano, amma a boye, aya jima a Abuja kwana biyu ya dawo Kano, yanzu haka ma ya dauko wata sabuwar fitsararriya daga Kasar Nijer.

Sannan batun garkuwa da Safara’u da na fadi hakane tabbas, ina da dalilai na da zasu tabbatar da wannanmugun halitta yayi garkuwa da Safara’u ta hanyar
yaudara, ya cutar da ita ta hanyar koya mata shan miyagun kwayoyi, ya take mata hakkinta, sannan yaci zarafinta, duka ina da dalilaina na fadin haka.

Idan sanaa ce nufinsa, ai yana da kanwa tana gidansu a garin Zaria jihar Kaduna, ya je ya daukota mana, amma sai ya yaudari ‘yar mutane ya lalata mata
rayuwa, suka dawo suna kokarin bata tarbiyyan al’ummar Musulmi, shi dan gidan uban waye ne a Nigeria da ba za’a kalubalanceshi ba?

Wannan Shine Abunda Mai Magana Datty Assalfy Ya Fada Biyo Bayan Wannan Abu Da Matashiyar Mawakiyar Takeyi Dasuke Janyowa Cece Kuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button