Abinda ya sa nake son Jarumi Rabi’u Rikadawa – Cewar Ladidi Tubless

Abinda ya sa nake son Jarumi Rabi’u Rikadawa – Cewar Ladidi Tubless ta bayyana wanda take son a Cikin jaruman kanywood wato Rabi’u rikadawa

 

 

Ta bayyana yadda ta fara shirin fim tun daga makaranta lokacin ana hada ‘yan shirye-shirye har Ubangiji ya yi zata ci abinci da harkar.

 

 

 

Yayin da aka tambayeta fim din da tafi so, ta ce duk fina-finanta tana matukar son su musamman wadanda ta kashe kudadenta wurin shirya su da kuma wadanda aka nemi ta yi su saboda ta karu kuma tana matukar alfahari da su.

 

 

 

Ta kuma hori matasa na masana’antar da su kasance masu neman ilimi ko da kuwa ba neman aiki za su yi da shi ba saboda akwai lokacin da zai zo wanda in har babu ilimi ba za a yi da mutum ba.labarunhausa na tattara labarai.

 

 

An tambayeta namijin da ta fi so a masana’antar Kannywood inda ta kada baki ta ce:

 

 

“Wanda na fi so a cikin mazajen fim, Alhaji Rabi’u Rikadawa, Dila wato Baba Dan Audu. Ai shi kamar dan uwana ne, yayana ne, aboki na ne kuma duk muna tare.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button