Kalli yadda wakar Ado Gwanja ke cigaba da rikita mata a TikTok

Sabuwar wakar Ado Gwanja na cigaba da rikita matan arewacin Nigeria musamman bayan gurfanar da mawakin a gaban kuliya da wani lauya yayi

 

 

Ado Gwanja dai na cigaba da Shan caccaka kan sabuwar wakar sa wadda ya raira Mai suna chass lakabin asosa inda mahukinta ke ganin cewa wakar Bata dace da asake ta ba

 

 

Sai dai Kuma bayan ja inja da mawakin sukayi da wasu lauyoyi , mawakin dai ya bar garin inda ya tafi Lagos don hadewa da fitacciyar jaruma Kuma mawakiya safarau lakabin saffa da Kuma Mr 442

 

 

Wannan hade watasu ta matukar tada hazo ganin yadda safaa din ke sheke ayar su babu kakkautawa, Gwanja dai ya saki wakar tasa ne a garin Lagos sakamakon Hana shi sakin ta da akayi a garin Kano

 

 

Bayan saki wakar ne dai shugaban tace fina finai na jihar Kano Ismail Afakallah Ahmad Muhammad ya shaidawa manema labarai cewa zasu nemeshi a koina yake Kuma su gurfanar dashi agaban kotu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button