Da Duminsa: Ado Gwanja Ya Saki Wakar Cassss

Da Duminsa: Ado Gwanja Ya Saki Wakar Cassss

Dukda Barazanar Gurfanar Dashi a Gaban Hisba, Fitaccen Mawaƙi Ado Isa Gwanja ya saki wakar Casss.

 

 

 

Ado Gwanja ya saki wakar ne a daren yau, kwana ɗaya bayan da wani lauya yai barazanar maka Hisba kotu idan bata dakatar dashi daga fitar da wakar ba.

 

 

Idan baku manta ba wani lauya Mai suna Barr. Badamasi Sulaiman Gandu ne yayi barazanar maka hukumar hisba ta jihar kano a gaban kotu matukar ta gaza dakatar da shahararren mawakin matan nan wato Ado Isa Gwanja daga fitar da wata Sabuwar waka da yayi Mai suna Casss.

 

 

 

 

A safiyar Laraba ne, Barista Badamasi Silaiman Gandu ya bayyana cewa, tuni ya aike da takardun gargadi na kwana uku ga hukumomin HISBA da hukumar Shari’a ta jihar kano domin su gaggauta dakatar da mawaki Ado gwanja daga fitar da sabuwar wakarsa mai suna Casss, kamar yadda Kadaura ta jiyo.

 

 

 

Barr. Gandu Wanda ya zargi mawakin da yin amfani da kalaman da basu dace ba acikin wakokinsa, yace barin irin wadannan wakokin a cikin al’umma zai kawo cikas wajen tarbiyyar yara masu tasowa.

 

 

Lauyan yace kamata ya yi gwamnatin jihar Kano ta dauki mawakin aiki a karkashin hukumar HISBA domin yin amfani da hikimarsa wajen fadakar da al’umma sabanin yadda yake amfani da hikimar ta wata hanya daban.

 

 

 

Sai dai a Martanin Ado Gwanja yace tun kafin a haife shi ake wakar Asosa dan haka karya ne ace wai wakar sa ce zata rusa tarbiyya.

 

 

Kwatsam a daren jiya mawakin ya saki wakar a shafin sa na YouTube, munyi kokarin tuntubar mawakin don jin ko meya sa ya saki wakar ana tsaka da cece kuce kanta sai dai bai samu ya daga wayar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button