Bana jin dadin yanda kananan yara ke aikomin da sakon soyayya – Hadizan Saim

Bana jin dadin yanda kananan yara ke aikomin da sakon soyayya – Hadizan Saima

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Muhammad da aka fi sani da Hadizan Saima ta bayyana cewa abinda ke fata mata rai shine irin yanda zaka ga yaro karami sai ya rika aika mata da sakon cewa yana sonta.
Ta bayyana hakane a hirar da tai cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na BBC hausa inda ta amsa tambayoyi da dama da suka shafi rayuwarta da kuma sana’arta.

 

 

Da take amsa tambayar wanene bazawarinta a Kannywood, Hadiza ta yi dariya inda tace da ba zai fadu ba kuma da tsada.
Da aka tambayeta da za’a canja mata kasa ina take so? Sai ta bayyana cewa Kasar Saudiyya,ta kuma ce bata taba zuwa Saudiyya ba.

 

 

 

 

An tambayi Hadiza shin talaka kamar Kamaye ko me kudi kamar Dangote, wanne zata zaba? Sai ta bayar da amsar cewa ai babu me son wahala.

 

 

Hadiza ta amsa tambayar cewa wanene Saurayinta na farko da cewa an dade kuma ba zata iya tunashi ba ko kuma a shekaru nawa yace yana sonta ba.

 

 

An tambayeta ko tana samun sakonni da basu da dadi, tace ba sosai ba amma wanda yafi damunta shine kaga karamin yaro wanda ta isa ta haifeshi ku kuma kani yace yana sonta.
Hadiza ta bayyana cewa bata da ranar Daina yin fim.

 

 

A karshe, Hadiza ta baiwa ‘yan mata shawarar su bi iyaye su kuma nemi sana’a,idan miji ya zo a yi aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button