Zaa gurfanar da fitaccen jarumi kannywood Ado Gwanja a gaban kotu bisa zargin sa da Bata tarbiyyar mata

 • Tun bayan sakin sabuwar wakar sa Mai suna chass , Al umma da dama na nuna rashin Jin dadin su kan irin Wakokin da mawakin ke saki ta rashin tarbiyya

   

   

  Ado Gwanja dai ya saki sabuwar wakar sa ne a Yan kwanakin Nan Wanda wakar take cigaba da tayar da hazo musamman ga iyaye kan wakar da kalaman da mawakin yayi amfani dasu a cikin wakar irin ta rashin tarbiyya

   

   

  Wani rahotoh da muke samu dai ya nuna cewa an Kai fitaccen mawakin Kuma jarumin Kara gaban lambar daya na jihar Kano watoh gomna Kano Abdullay ganduje

   

   

  Rahotanni sun Kara da cewa jarumin Ado Gwanja ba daf da gurfana a gaba kotu inda za a Yi karar da kan Bata tarbiyya mata musamman hausawa

   

   

  Wannan dai ya biyo bayan sakin wakar sa Mai suna chass inda tuni dai wakar ta fara rikita Hadi da tunzira mata musamman a kafafen sada zuminta irin su TikTok, Facebook da dai sauran su

   

   

  Wannan wakar tasa ta biyo bayan wakar sa Mai suna warrr wadda ta rikita mata a kwanakin da suka gabata Wanda wasu rahotanni sun nuna ma cewa tsohuwar wakar tasa tayi sadadiyyar rabuwar auren wata mata

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button