Maryam Yahaya Na Cikin Tsaka Mai Wuya / mama Daso Taja Kunnen Matan Kannywood

Mu Kiyaye Sa Sutura Mai Bayyana Tsiraraici – Das0 Ga Matan Fim domin wani abu data gani na Maryam Yahya tana yi da kuma irin shigar da suke yi

FITACCIYAR jaruma Saratu Giɗaɗ0 (Das0) ta jan hankalin ‘yan matan masana’antar finaginan Hausa na wannan zamani a kan saka ire-iren sutura masu nuna surar jikin su.

Das0 ta wannan tsokacin ne lokacin da aka ba ta damar yin magana a taron saukar Alƙur’ani da yi wa ƙasa addu’a wanda mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) ya shirya a Kano a shekaran jiya Litinin.

Jarumar barkwancin ta yi amfani da wannan damar ta ce, “Ya kamata mu mutunta kan mu a duk inda mu ke. Haka kuma don Allah mu kiyaye saka suturar da zai nuna tsiraicin mu, musamman ‘yan matan mu na wannan zamani. Hakan ba daidai ba ne, mu kiyaye.”

Daso ta yi addu’ar Allah ya ƙara kare su daga sharrin mahassada da maƙiya Allah kuma ya basu ikon aikata dai dai ya basu ikon gyara ba dai dai ba

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button