Ya Kamata Ummi Zee,zee Ta Zama Izna Ga Rayuwar Safara’u

Ummi Zeezee ma ta yi ta gama: Martanin jama’a ga Safara’u bayan yin hoto da 442 da gajeren wando

 

Wasu sabbin hotuna da tsohuwar jarumar Kannywood kuma mawakiya, Safiyya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ko Safaa, sun janyo cece-kuce a Instagram.

 

A hoton an ganta sanye da dogon wanda da karamar riga kanta a bude yayin da shi mawaki 442 din ke sanye da riga da gajeren wando.

 

 

Sun jingina da juna ne tamkar mata da miji ko kuma ‘yan uwan juna duk da dai kowa ya san ba su da alakar jini.

 

 

 

Nan da nan mutane su ka hau tsokaci karkashin wallafar tata su na maganganu har wasu ke cewa ko tsohuwar jaruma Ummi Zeezee ta yi nata zamanin ta gama.

 

 

Idan ba a manta ba, Ummi Zeezee ta yi soyayya da mawakin kudu, Timaya, wanda har a lokacin aka dinga cewa za su yi aure duk da shi ba musulmi ba ne.

 

 

Bayan sun gama yawata duniya ya dawo ya bar ta ba tare da ya aure ta ba wanda hakan ya kara tayar da kura har aka dinga cewa an san hakan za ta faru don yaudarar sun san ze yi.

 

 

Ta boye na wani lokaci wanda aka dena duriyarta daga bisani kwanaki ta bayyana cewa tana so ta halaka kanta.

 

 

Hakan yasa mutane ke ta alakanta rayuwar Safara’u mai bin mawaki 442 da kuma Jaruma Zeezee da ta gama bin Timaya ya zo ya bar ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button