Wani Matashi Ya Nemi Auren Safara’u Duka Da Fitsarar Da Take Yi A Duniya

Kunga wani ya taro March ko? To ina son ku isar masa da wannan saƙon, ida yaga zai iya cike dukkan ƙa’idoji da sharuɗɗan da na gindaya to na yarda zan aure shi ga su kamar haka.

 

Zan aureka idan ka cika dukkan waɗannan sharuɗɗun da farko

 

 

Na farko dole mu yi yarjejeniya a rubuce kasa hannu nima in sa, cewar bayan ka aureni za ka barni in ci gaba da sana’a ta wato rawa da waƙa.

 

 

 

Na biyu idan ba za ka barni ba to za ka bani jarin naira miliyan 100 domin in fara zuwa Dubai ina siyo kaya ina siyarwa.

 

 

Na ukku dole ka bani kyautar gida a Kaduna da Abuja da kuma motar hawa wacce ta kai darajar naira miliyan 15.

 

 

Idan ka ga za ka iya to ka ajiye min number wayarka zan kira ka.

 

 

Don Allah masoyana ku taya ni tura wannan saƙon zuwa sauran groups don jama’a su ƙara gani ko zan samu mai cika waɗannan sharuɗɗan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button