Innalillahi Video Yadda Wata Budurwa Ta Rasa Kafa Yayin Murnar Candy

Inna lillahi wa’inna ilaihin raji’un: Wannan baiwar Allah mai suna Fateema kunga yadda Allah ya mayar da ita ciki sati guda, yanzu kwana 7 da suka wuce ba haka take ba.

Wanna abu ya faru ne a wasu yan kwanaki da suka gabata wanna lamarin ya bawa mutane da dama tausayi wanna dalibar Fatima sai dai kawai ace Allah ya kyauta gaba

 

Budurwa ce kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa ga ilimin addini da na zamani ga haƙuri ga son jama’a, ta kammala zana jarabawar ta na NECO sun fito ana murnar gama makaranta wani ɗalibi yana ganganci da mota.

 

 

 

 

Kawai sai ya yo kanta ya take mata ƙafa yanzu haka an yanke mata ƙafar dama dole sai dai ta ƙare rayuwarta ta duniya a haka, muna fatan Allah ya kiyaye gaba kuma ya bata lafiya, ya kawo mata mijin aure nagari wanda zai tausaya mata ameen

 

 

Lallai ya katama hukuma ta san yadda zata rinka tsara yanayin ladabai yayin kammala karatu domin gujewa irin wanna yanayin da aka saka wanna baiwar Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button