An Taɓa Ɗaure Min Hannu Aka Jefa Ni Cikin Rafi Saura Ƙiris Kada Ya Yi Kalace Da Ni

Kannywood: An Taɓa Ɗaure Min Hannu Aka Jefa Ni Cikin Rafi Saura Ƙiris Kada Ya Yi Kalace Da Ni, Baba Musa

 

 

Jarumin fina-fina, Musa Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Baba Musa a ‘Kwana Casa’in’ ya bayyana cewa rashin hadin kai ne babban kalubalen da ke damun Kannywood

 

 

Baba Musa cikin wata tattaunawa da aka yi da shi ya magantu kan abin da ba zai taba mantawa inda ya ce an taba jefa shi cikin rafi a daure kuma kada ta nufo inda ya ke

 

 

Tsohon Jarumin Fina-Finan ya kuma ce akwai banbanci tsakanin jaruman yanzu da na zamaninsu amma yana da yakinin cewa za a samu cigaba a masana’antar

 

 

Musa Muhammad Abdullahi, da aka fi sani da Baba Musa, tsohon jarumi ne da ya fara fitowa a fina-finai tun kafin a kafa Kannywood kuma a yanzu yana cikin taurarin dirama mai dogon zango mai suna ‘Kwana Casa’in

 

 

 

 

A hirar da aka yi da shi, ya yi magana kan batutuwa da dama da suka shafi karatunsa, aikinsa, masana’antar fim na Kano da Kaduna, sauye-sauye da aka samu da kallubalen da ake fuskantar dashi

 

 

An masa tambaya kan kallubale mafi girma da ya taba fuskanta kawo yanzu, kuma ya kada baki ya ce

 

 

“Na ga abubuwa da dama a harkar fim. Akwai fim din da muka yi inda wasu mata suke amfani da hijabi wurin aikata abu mara kyau. A lokacin, akwai tsatsaurin ra’ayin addini.

 

 

Wasu masu tsaurin ra’ayin suka ce dukkanmu jaruman a halaka mu. “Wata rana ina tafiya a Tundun Wada Kaduna, wani cikin matasan ya gane ni ya sanar da sauran, suka taho da nufin kai min hari. Amma na yi sa’a wasu matasa suka kare ni kuma yan sanda suka kama su

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button