YAN AREWACIN NIGERIA SUN GAJI DA MULKIN BABA BUHARI

Yan Nigeriya sun matsu sauke Buhari
Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ɓangaren rinjaye a majalisar dattijan Najeriya ce ta soma gabatar da batun neman a tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari, muddin bai ɗau matakin kawo ƙarshen matsalolin tsaro ba.

Sanata Shekarau wanda mamba ne a kwamitin tsaro na majalisar dattijan Najeriya ya shaida hakan ne a wata hira ta musamman da aka yi

Sanatan ya ce a lokacin zaman da majalisar ta yi kan halin da Najeriya ke ciki na taɓarɓarewar tsaro an shafe sama da sa’a uku ana dambarwa, kowa na tsokaci da kawo nasa ra’ayi, har aka kai ga matsayin neman a tura takardar tsigewa zuwa ga shugaba, Muhammadu Buhari bayan ba shi wa’adi.

Wannan batu na tsige Buhari kan matsalar taɓarɓarewar tsaro ya jawo yamutsi a zauren majalisar dattawan sakamakon zazzafar muhawarar da ‘yan majalisar suka yi a tsakaninsu.

APC ya fito’
Malam Ibrahim Shekaru ya ce ba zai ambaci suna ba, amma dai mutum na farko da ya soma gabatar da wannan batu na neman tsige shugaba Buhari a majalisa ɗan APC ne, haka zalika mutum na biyu da ya goyi-bayansa kafin sauran mutane shi ma ɗan APCn ne.

Ya ce “Ba zan soma kama sunan kowa ba amma wallahi ina tabbatar ma ka cewa wanda ya soma tashi ya ce a rubutawa shugaban ƙasa takardar tsigewa wallahi ɗan APC ne, wanda ya goyi-bayansa ma wallahi ɗan APC.

“Wannan zama ne na ɗaki da zama ne na zauren majalisa da kowa ya shaida, har da ‘yan jarida. Ina son mutane su san cewa maganar kalmar a tsige shugaban ƙasa daga wajen APC ta fito ba ɓangaren masu hamayya ba, su suka faɗi abin su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button