Tsohon Abokin Dan Kwallon Nijeriya, Ahmed Musa Tun Na Kuruciya Na Cigiyarsa

Tsohon Abokin Dan Kwallon Nijeriya, Ahmed Musa Tun Na Kuruciya Na Cigiyarsa

Tsohon abokin dan kwallon Nijeriya Ahmed Musa wanda suka taso tun yarinta a Layin Giginya dake Unguwar Bukur a garin Jos yana cigiyar aminin nasa biyo ya rasa yadda zai yi su yi ido hudu.

Mutumin ya ce Ahmed Musa ya fi saninsa da Gwamna, wato sunan da ake kiransa da shi a lokacin, sannan kuma ya bayyana cewa bacci ne kawai yake raba su da Ahmed Musa a lokacin kuruciyar su, inda a wasu lokutan ma suna kwana ne a gidajen juna, wato wani lokaci ya kwana a gidan su Ahmed Musa, shi ma kuma Ahmed Musa ya kwana a gidansu.

Saidai rahotanni sun nuna cewa Gwamna yana cikin kuncin rayuwa wanda yake bukatar tallafi.

Ya ce ya fi wata biyar yana ta kokarin ganin yadda za a yi a hada shi da Aminin nasa, amma burinsa har yanzu bai cika ba, don haka ne ya ce bari ya biyo ta kafar sadarwa ko Allah zai sa Ahmed Musan ya gani ya neme shi.

A cikin wadannan hotunan za a iya ganin Ahmed Musa da Gwamna, inda aka sa musu alama akansu.

Don haka ne ma Gwamna ya ajiye lambarsa don kira kai tsaye idan Allah ya sa Ahmed Musan ya ci karo da labarin; 07069204905

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button