Saratu Dan-Azumi, karamar yarinyar da ta bar makaranta kuma take iya lissafi kamar kwamfuyut

Saratu Dan-Azumi, karamar yarinyar da ta bar makaranta kuma take iya lissafi kamar kwamfuyuta, ta sake samu an dauka nauyin karatunta Wannan daukar nauyin karatun da aka yi a cikin kwanakin nan ya zo ne daga Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment AGILE shiri ne na bankin duniya kuma ya nemo tare da samo yarinyar a Kano tare da daukar nauyin karatunta

Gaya, Kano – An sake daukar nauyin karatun Saratu Dan-Azumi, karamar yarinya daga jihar Kano wacce ta kware a lissafi.
Domin ta samu ingancen katura domin kuwa barin irin wanna yaran babu ilimi a Sara ne a cikin al’umma

A cikin kwanakin nan ne aka gano cewa yarinyar da ta bar makaranta amma take iya sarrafa lambobi kamar kwamfuyuta hakan yasa yanzu an maida ita domin ci gaba da karatun ta har zuwa inda Allah ya sa

Wannan daukar nauyin karatun ya zo ne daga Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment, shirin da bankin duniya ke taimakawa.

Gidauniyar Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban kasa ne ya fara daukar nauyin yarinyar domin ta samu ilimin da ya dace wanda a da bata sami wanna damar

A yayin martani kan labarin me dadi, Saratu ta sanar da cewa ta bar makaranta lokacin tana aji hudu na firamare saboda zaluntarta da ‘yan ajinsu ke yi. Tace ta shirya komawa makaranta amma ba za ta koma tsohuwar makarantarta ba inda ‘yan ajinsu ke cin zalinta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button