Peter Obi Ba Zaiyi Nasarar Lashe Koda Rabin Jihar Nasarawa Ba – Inji Deji Adeyanju

Shahararren Dan gwagwarmaya a Najeriya Deji Adeyanju ya bayyanawa magoya bayan Dan takarar Shugaban Kasa Peter Gregory Obi cewa Dan takarar da suke goyon baya ba zaiyi nasarar lashe zaben jihar Nasarawa ba.

A cikin wani jawabin da Deji Adeyanju ya fitar ya bayyana cewa ga magoya bayan Peter Obi cewa zai karyamusu zuciya akan maganar da zai gayamusu wadda ta shafi Dan takarar da suke goyon baya.

Mista Adeyanju ya kara jaddadawa magoya bayan Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour Party cewa kaso 90 daga cikin wadanda suka fito zanga-zangar an biyasu ne sannan kuma ba zasu zabe shi ba.

Deji Adeyanju ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter jim kadan bayan da wasu magoya bayan Peter Obi suka fito suna zanga-zanga a jihar Nasarawa sannan suka nuna goyon baya ga tafiyar Obidient wadda masu goyon bayan Peter Obi keyi.

Wannan ba shine karon farko da Deji Adeyanju ke sukar Peter Obi domin ya fusata magoya bayansa dake amfani da shafin Twitter ba.

An zargi magoya bayan Peter Obi da sukar wadanda basu goyon bayan Peter Obi da kuma yin barazana ga wasu daga cikinsu.

Saidai duk da hakan, bai hana Deji Adeyanju ya cigaba da sukar Peter Obi da magoya bayansa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button