Mahaifiyata Ta Sare Min Hannaye Haka Siddan – Budurwa

Wata budurwa mai suna Gloria Smart, da ke zaune a yankin Ezhionum na Jihar Delta, ta bayyana yadda mahaifiyarta ta tasamma hallaka ta ba tare da dalilin komai ba.

Mahaifiyar ta kai mata sameme ne da adda, inda akai ba ta yi nasarar kashe ta ba.

Da take zantawa da manema labarai, budurwar mai shekarun 21, ta bayyana cewa, mahaifiyarta ce ta sare mata hannaye biyu gami da kekketa mata fuska da adda.

Ta bayyana wa manema labarai cewa har yanzu bata san laifin da ta yi wa mahaifiyarta da take yunkurin kashe ta ba.

Ta ce abin da ya faru da ni abu ne da ban taba tsammani ba, domin ko mahaifiyata ce da kanta ta sare min hannaye gami da kekketa min fuska da adda.

Da aka tambaye ta game da yadda lamarin ya faru sai ta ce, “Abin da zan iya tunawa shi ne, wata rana na shiga yin fitsari ban san mamata tana rike da adda ba, kawai sai na ji an fada ni da sara ko ta ina.

“Ihun da nake yi ne ya sa mahaifina ya kawo min dauki, ko da ya zo kaina lokacin ta gama sassara ni na fadi a sume.

“Abin da ban sani ba shi ne, ashe shi ma baban nawa ya so ya sassara mahaifiyar tawa, bayan da na farka ake gaya min.”

“An yi nasarar hana shi ne aikata hakan ne yayin da aka ji yana kururuwar neman a masa kawo dauki, zuwansu ya taimaka, yayin da a bangare guda kuma aka tasa keyar mahaifiyar tawa zuwa ofishin jami’an tsaro,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button