Luguden Ruwan Wuta Ya Kashe Kwamandan Boko Haram A Borno

Dakarun rundunar sojin saman Operation Hadin Kai, sun kashe wani kasurgumin kwamandan Boko Haram, Alhaji Modu, wanda aka fi sani da Bem Bem.

An kashe Modu ne tare da wasu ‘yan ta’adda 27 a jihar Borno.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babban hafsan hafsoshin sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao, ya bukaci kwamandojin rundunar sojin sama ta Nijeriya, da su nuna rashin tausayi, da kuma tabbatar da sun yi amfani da ruwan wuta a kan ‘yan ta’addan da ke barazana ga tsaro a kasar.

An kashe ‘Bem Bem’ da mayakansa a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta, 2022, sakamakon wani hari da jiragen yakin soja suka kai a kan tsaunin Mandara da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.

Wani rahoton leken asiri da Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ‘yan tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya samu daga manyan majiyoyin soji da aka bai wa LEADERSHIP a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce wani binciken barnar da aka yi a yakin ya nuna cewa harin jirgin ya yi tasiri a kan mutane da dama. An kashe masu mayakan yayin da wasu suka samu munanan raunuka.

Majiyoyi sun ce harin ya biyo bayan sahihan rahotannin sirri da ke nuni da cewa mayakan na Boko Haram na haduwa a wani waje da nufin kai hare-hare.

‘Bem Bem’ ya kasance sanannen dan tada kayar baya wanda ya taso daga dan fashi da makami jagoran Boko Haram.

Ya taka rawa wajen gudun hijirar mutane da dama daga garin Bama a shekarar 2014 da kuma kashe daruruwan mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button