Kidayar ‘Yan Nijeriya Ta 2023: Shugaba Buhari Zai Bude Taron Masu Ruwa Da Tsaki

Shugaba Muhammadu Buhari zai bude taron masu ruwa da tsaki kan kidayar da za a gudanar ta al’ummar Nijeriya da matsugunansu a 2023.

Taron wanda hukumar kidayar al’umma ta kasa ce ta shirya, za a gudanar da Shi ne a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Villa, Abuja.

Hukumar kidayar, reshen Majalisar Dinkin Duniya ce ta tallafa don gudanar da taron, musamman domin a samu yin aikin na kidayar a cikin nasara.

A cilkin sanarwar da Dakartan hulda da jama’a na hukumar, Dakta Isiaka Yahaya ya fitar ya sanar da cewa, taron zai taimaka wajen wayar da kan al’ummar Nijeriya kan yadda za a gudanar da kidayar, ciki har da dabarun zamani da za a yi amfani da su da lokaci da kuma neman taimakon masu ruwa da tsaki.

Ana sa ran manyan jami’an gwamnatin tarayya da na jihohi da sarakuna da manya daga kafafen yada labarai da kungiyoyi masu zaman kansu da malaman addinatai da kungiyoyin mata da na matasa da sauransu, za su halarci taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button