Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya rigima ta barke tsakanin Sadiya Haruna mai kayan mata da kuma jarumar masana’antar kannywood

Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya rigima ta barke tsakanin Sadiya Haruna mai kayan mata da kuma jarumar masana’antar kannywood Teema makamashi, wanda har abin nasu ya kai tonawa juna asiri.

To a yanzu ma rigimar tasu tana neman dawowa danya bayan da aka sace wani kanin Sadiya Haruna mai suna besty, wanda har Sadiya Haruna take fadin cewa zata yi karar su Teema makamashi.

Bayan haka Sadiya Haruna ta fadi abubuwan su Teema makamashi suke mata wanda hakan yana takurawa rayuwar ta.

To a yanzu kuma mun sami wata bidiyo daga tashar Kundin shahara dake kan manhajar Youtube, inda muka ga Fati Slow wanda take goyon bayan Teema makamashi tana karyata abubuwan da Sadiya Haruna take fada akan Teema makamashi.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji yadda Fati Slow take karyata Sadiya Hatuna akan abubuwan da take cewa Teema makamashi ta yi mata

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button