Gembu Taraba: Mota biyar ne ta faɗi a wannan haƴan cikin mako guda– inji Abdullahi Buba

Gembu Taraba: Mota biyar ne ta faɗi a wannan haƴan cikin mako guda– inji Abdullahi Buba

Daga Abdulaziz ibrahim

Gurɓacewar hanyar gembu na ƙaramar hukumar Sardaunan jihar Tarab, na cigaba da yiwa Yankasuwa, direbobi dama fasinjoji barazana ta hanyar laƙume rayuka da dama, wanda a kowace mako akan samu sama da mota huɗu ke faɗuwa makil da hatsi, kayan masarufi dama kayayyakin aiki na yau da kullum.

Gembu ta kasance gari ne dake kan tsauni Wadda akanyi tafiyar Sa’o’i kamin isa garin kuma tana da albarkatu da dama kama daga ƙyakyawar yanayi da kuma kasan noma mai inganci. Kasancewar sanyi a yankin yasa garin tayi shura wajen samar da ƴaƴan itatuwa wadda suke sadarwan shi izuwa wasu yankuna domin saida shi.

Sai dai a yanzu a iya cewa garin na gap da daina safarar waɗannan kayan marmari duba da irin gurɓatar ta hanyar tayi.

Abdullahi Buba, ɗan kasuwa dake safaran kaya daga wasu yankuna izuwa gembu, ya bayyana wa wakilin mu cewa matsalar wannan hanya tun ba a haifeshi ba ake fama da ita.

Abdullahi Buba yace “babu wani rawa da muka gani gwamanti ta takka kan gyara wannan hanya, sai dai akwai yan siyasar da suka mana alƙawarin idan har mun marra musu bayya suka ci zaɓe zasu gyara mana hanyan. Senator Marafa Bashir na daga cikin waɗanda suka mana wannan Alƙawarin”.

“kuma Wannan hanya ne aka ce mana kamfanin Man fetur ta Najeriya NNPC da ma hukumar rayya arewa Maso gabas wato North-east Development Commission ta ɗauki alhakin gayarawa wadda a kwanakin muka ga wasu turawa suka zo amma har izuwa yau ba mu sake su a idanun mu ba kuma mun samu labarin an mallakar wa yan kasuwa NNPC, to kome makomar gyaran wannan hanya”.

“ Motoci sama da guda biyar ne suka faɗi a cikin satin nan kuma Ni ma lallacewar hanyan ne yayi sanadiyar faɗuwan mota, wannana Allah ya kiyaye direban ya kai motan ta dutse idan bahaka mudin ta koma baya babu wanda zai tsira daga kan direba da kayyan gabaɗaya” inji Abdullahi Buba.

Abdullahi Buba ya ƙara da cewa“ suna ƙura ga gwamnati da ma mahukunta ta su tausaya musu su kawo musu ɗauki, kuma suna cigaba da addu’a domin Allah ya sa ayyi musu wannan aiki cikin gaggawa”.

Shima wani direban motar ɗaukar kattako ya bayyana cewa sau uku kenan motarsa take faɗuwa a wannan hanya, kuma duk cikin wata ɗaya.

Abin tambayar anan shine, ko yaushe gwamnatin Najeriya zata kawo ƙarshen wannan matsala da aka shafe shekaru arru arru ana famma??

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button