Fati Slow-motion ta yi kacakaca da teema makamashi, inda tace kada ta bari su yi tone-ton

Fati Slow-motion ta yi kacakaca da teema makamashi, inda tace kada ta bari su yi tone-tone – Hakan ya biyo bayan tonon silili da teema ta yi wa yan matan Kannywood kan Rahama Sadau, harma ta kira wasun su da yan madigo

Yan Kannywood dai sun caa a kan Rahama bayan bayyanar hotonta da ya janyo batanci a kan Annabi Jarumar Kannywood wacce aka fi sani da Fati Slow-motion ta mayar da martani ga teema makamashi a kan fallasar da ta yi wa yan matan Kannywood da suka caccaki Rahama Sadau kan shigar da tayi

Fati ta gargadi teema makamashi a kan ta kiyaye ta don kada ta bari su yi tone-tone, idan ba haka ba sai ta kwance mata zani a kasuwa domin kuwa ita bata tsoron ayi uwar watsi da ita

Ta kuma shawarceta da ta je ta rungumi aurenta maimakon ganinta da ake yi a tsakiyar maza a koda yaushe lallai fati slow ta maida martani a kan abun da teema makamashi take fadi a kan ta dama sauran yan kanywood

Lallai wanna abu da ya faru da teema makamashi ita ta jawo ma kanta domin kuwa tun baya ita fati slow ta bayyana kada ta bari su fara Irin wannan abun da ita domin bazata barta ba sai ta tona asirin ta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button