AMBALIYA: Al’ummar Yankin Kirfi Na Neman Daukin Gaggawa Daga Gwamnatin Bauchi

A iya abinda ido ya iya gani na tashin hankali da firgici sakamakon ruwan sama da ya mamaye tare da ambaliyan da ya yi sanadin share gidaje gonaki dabbobi da kasuwanni, da hakan ya tilasata wa dubbanin mazauna wannan yankunan da abin ya shafa yin hijira .

A daidai irin wannan lokaci da ibtila’in ambaliyan ruwan sama ya auku a sassan jihar Bauchi, karamar hukumar Kirfi ita ce yankin da wannan lamari ya fi muni, da yawan mutane ruwan ya shafe muhallan su ya shafe gonakin su ya tafi da dabbobinsu.

Jarabawar ta yi girmar da ba dukkan kirji ne zai iya dauka ba, ala tilas mata da ‘ya’yan su sun koma kwana a Ajujuwan makaranta ba tare da tabbacin abinda za su kai bakin su ba, haka suturar da za su sa a jikin su ta gagara balle batun shimfidin da za ayi amfani da shi a makwanci.

Gudumuwar gwamnati da ‘yan siyasa abu ne da za mu iya kiran sa da tallaafi irin na gaggawa, hakan abune mai kyau. Mu kuma a yanzu muna magana ne kan batun makomar wadanda ibtila’in ya shafa kama daga muhallan su da kuma duba batun hanyar abincin su na yau da gobe.

Daga Alhaji Abbas Baffah Cheledi Jihar Bauchi, Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button